Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

30 Mayu 2022

11:19:21
1262222

​Masar: Wata Kotu Ta Yanke Hukuncin Daurin Shekaru 15 Kan Tsohon Dan Takarar Neman Shugabancin Kasar

Wata kotu a birnin Alkahira na kasar Masar ta yanke hukuncin daurin shekaru 15 kan Abdulmumini Abul-Futuh, tsohon dan shekarar neman shugabancin kasar daga kungiyar yan uwa musulmi wacce gwamnatin kasar ta haramta.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - bayyana cewa Abul-futuh dan shekara 70 a duniya yana fama da cututtuka da dama a lokacinda kotun ta yanke masa hukuncin shekaru 15 na zaman kaso, saboda laifin yada labaran kariya da kuma yunkurin juyin mulki a kasar.

Labarin ya kara da cewa Mohammad Al-Qassas ya tashi da shekaru 10 a gidan kasu. Sai kuma Muhammad Azzat wandakotun ta daure shekaru 15 shima.

342/