Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

30 Mayu 2022

11:17:14
1262219

​Sudan Ta Mayar Da Martani Kan Kalaman Habasha Game Da Madatsar Ruwan Renaissance

Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta fitar da wata sanarwa inda ta yi tsokaci kan kalaman Habasha dangane da madatsar ruwa ta Renaissance.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta ce kalaman daraktan madatsar ruwa ta Grand Ethiopian Renaissance Dam, Kifle Horo, kan cewa ana sa ran cike madatsar ruwan a cikin watannin Agusta da Satumba masu zuwa, hakan ya kara zaman dar-dar a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma hakan ya a cewar sanarwar ta Sudan, ya keta yarjejeniyoyin da suka gabata.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta yi kira ga jami'an kasar Habasha da su daina irin wadannan kalamai da suka saba wa bin ka'idojin diflomasiyya, tare da fifita hanyar tattaunawa a matsayin zabin da yafi dacewa wajen warware takaddamar da ke tsakanin kasashe uku kan madatsar ruwa ta Renaissance.

Ma’aikatar Harkokin wajen Sudan ta bayyana cewa, ta bi wadannan kalamai cikin damuwa, inda ta yi nuni da cewa, daraktan kula da madatsar ruwa ta Renaissance Dam a cikin bayanin nasa ya yi biris da dukkanin abubuwan da aka cimma matsaya a kansu.

Haka nan kuma bayanin na Sudan na jaddada wajabcin bin yarjejeniyoyin da aka kulla da kuma tsarin shawarwarin da ke kiyaye 'yancin bangarorin uku, na Sudan, Masar da kuma Habasha, domin cimma daidaito kan rikicin madatsar ruwa ta Renaissance.

A wata sanarwa da daraktan aikin dam din na Habasha ya fitar a ranar Juma'a ya yi ikirarin cewa aikin cike madatsar ruwa zai iya shafan Masar da Sudan, amma duk da haka ya ce za a ci gaba da aikin a mataki na uku, wanda ya sa ran za a yi a watan Agusta da Satumba.

342/