Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

28 Mayu 2022

15:10:42
1261816

Iran Ta yi Tir Da Wasu Matakan Kasashen Turai A Bangaren Wasanni Da Hakkin Dan Adam

Kakakin gwamnatin kasar Iran ta soki lamarin kasar Kanada game da matakin da ta dauka na soke wasan sada zumunta da aka tsara za’a yi tsakanin ta da kasar iran , yace abin takaici ne yadda manofofin siyasa yake musu tasiri akan wasanni da kuma hakkokin dan adam

ABNA24 : Hukumar kwallon kafa ta kanada ta sanar da kulla yarjejeniyar yin aiki tare da hukumar kwallon kafa ta kasar iran ,inda aka tsara tawagar kwallon kafa na kasahen biyu za su buga wasan sada zumunta tsakaninsu a ranar 5 ga watan juni, amma kwatsan sai ga shit a sanar da soke wasan ba tare da wani dalili ba.

Ali Bahdori Jahromi ya fadi cewa soke wasan sada zumunta da tsakanin Iran da kanada da kuma dakatar da kasar rasha daga halartar duk wata gasa sun daga cikin misalan tarisin siyasa a harkar wasanni adadai lokacin da suke ikirarin yanci da rashin sanya siyasa a bangaren wasanni.

Daga karshe yace kasashen turai suna daga cikin wadanda suka fi yawan take hakkin bil adama a duniya , kuma suna nuna yin harshen damo game da abin daya shafi hakkin bil adama.

342/