Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

28 Mayu 2022

15:06:37
1261810

​Rasha Da China Sun Yi Fatali Da Daftarin Kudurin Amurka Kan Koriya Ta Arewa

A yayin kada kuri'a a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar jiya Alhamis, Rasha da China sun ki amincewa da daftarin kudirin Amurka na fadada takunkumin da aka kakabawa Koriya ta Arewa.

Kasashe 13 a majalisar sun kada kuri'ar amincewa da daftarin kudurin.

Daftarin kudurin ya kunshi yin Allah wadai da harba makami mai linzami da Koriya ta Arewa ta yi a ranar 24 ga Maris, da kuma wasu gwaje-gwajen makamai masu linzami da Pyongyang ta yi a baya-bayan nan.

Daftarin kudurin ya ba da shawarar rage yawan danyen mai da ake samarwa ga Koriya ta Arewa bisa ga kudurorin kasa da kasa, daga ganga miliyan 4 zuwa ganga miliyan 3.

Hakan na kuma daftrain kudirin ya hada da wasu takunkumai da dama kan kasuwanci da Koriya ta Arewa, baya ga takunkumi na kashin kai kan wani babban jami'in Koriya ta Arewa, wanda aikinsa ke da alaka da sa ido kan kera makamai masu linzami, da kuma daskarar da kadarorin wasu hukumomi 3 na kasar.

342/