Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

28 Mayu 2022

15:05:55
1261809

​Najeriya: An Gudanar Da Zabukan Fitar Da Gwani Na Gwamnonin APC

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta gudanar da zaben fitar da gwani na masu neman takarar mukamin gwamna a karkashin jam`iyyar a wasu jihohin.

Zaben dai ya gudana ba tare da hatsaniya ba a wasu jihohin, yayin da a wasu kuma an samu kace-na-ce tsakanin wasu `yan takara.

Haka nan kuma wasu gwamnoni sun samu damar yin nasarar takara a karo na biyu, yayin aka samun sabbin fuskoki a wasu jihohin musamman wadanda wa’adi na biyu na gwamnoninsu ya kare.

Duk da cewa zabukan sun gudana lami lafia, amma kuma wasu daga cikin ‘yan takara da ba su yi nasara ba, sun koka kana bin da suka kira magudi ko kuma nuna musu fin karfi.

342/