Shafin yanar gizo na Labarai ‘Afirka news’ ya nakalto Sall yana fadar haka a jawabin bude taron da ya gabatar a birnin Malabo na kasar Equatorial Guinea, inda kungiyar AU take gudanar da taronta na farko kan agaji a mahiyar Afirka.
Kafin haka dai shugaban kasar Equatorial Guinea’ Teodoro Obiang ne ya bude taron a matsayin kasa wacce ta ke daukan bakwancin manya-manyan tarurruka guda biyu. Dukkaninsu dangane fa yadda za’a shafi kan matsalar ‘yan gudun hijira da kuma ayyukan bada Agaji a nahiyar,
Shugaba Sally a yi alkawar bada dalar Amurla miliyon uku a matsayin tallafin kasar kan wannan lamarin.
An kiyasta cewa yawan yan gudun hijira a nahiyar Afirka a shekara ta 2020 ya kai miliyon 282 kuma akwai has ashen cewa wannan adadin zai kara a wannan shekara da ake fada da karancin abinci a duniya gaba daya saboda yaki a Ukrain da kuma matsalolin cutar Corona suka jawo.
342/