Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

26 Mayu 2022

20:09:19
1261288

Isra’ila Ta Sanar Da Alhakin Kisan Mamba A Dakarun Kare juyin musulunci Na Iran

Rahoton da Jaridar Newyork Times ta wallafa ya ce Haramatacciyar kasar Isra’ila ta shaidawa kasar Amurka cewa itace ke da alhakin kisan gillan da aka yi wa mamba a dakarun kare juyin musulunci na Iran Kanar Hassan Sayyad Khodaei annan birnin tehran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Dubun dubatan Alummar kasar iran ne suka halarci jana’izar babban jarumin, kuma sun gudanar da kwarya kwaryan zanga-zanga inda suke ta rera taken mutuwa ga Isra’ila da kuma yin kira da adauki fansar kisan gillan da aka yi masa.

Dama daga cikin jami’an kasar Iran da suka hada da Majid Mirahmadi mamba a cibiyar tsaron kasa nacewa babu shakka wannan kisan, aikin Isra’ila ne kuma yayi gargadin daukar fansa mai tsanani kamar yadda jaridar ta byyana.

Wani mai sharhi kan harkokin gabas ta tsakiya ya fadi cewa isra’ila ta yi wannan tsokanar ne domin matsin lamba kan bangarorin da ake tattaunawa kan shirin nukiliyar iran, ko kuma fusata iran ta mayar da martani yadda al’amura za su lalace, sai dai Iran ta na sanya hikima da hange nesa wajen tunkarar irin wadannan lamurra.

342/