Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

25 Mayu 2022

18:13:58
1260907

​Jagora: Ana Iya Warware Matsaloli Ta Hanyar Gwagwarmaya Da Himma

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyeed Aliyul Khaminaee ya bayyana cewa ana iya warware matsalolin da kasar take ciki a halin yanzu, tare da himma da kuma juriya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - nakalto jagoran yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a gaban yan majalisar dokokin kasar Iran wadanda suka kai masa ziyara a gidansa a yau Laraba.

Jagoran har’ila yau, ya bayyana cewa irin nasarar da mayakan Iran suka samu kan sojojin mamaya na Dasam Husain a ranar 24 ga watan Mayun shekara ta 1982 a garin Khorramshahr wani babban darasi ne a dukkan matsalolin da kasar take ciki. Ya ce mutanen da suka sami nasara a kan sojojin Iraki a farmakin baitul Mukaddasi a wancan lokacin, basu da wata korewa sosai a fagen yaki, amma himma da suke da shi da dogaro da kai ya kais u ga samun nasara a kan sojojin kasar Iraki yan Mamaya.

Daga karshe jagoran ya kammala da cewa, yaki baa bin jin dadi bane, amma kuma nasarar da IOran ta sami a yakin da ta fafata da gwamnatin Iraki ta lokacin ya zama abin farinci garesu. Kuma suna iya amfani da wannan himman wajen warware matsalolin rayuwan su a wasu fagagen.

342/