Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - NAN ya ce an rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar ce a gefen taron kafafen yada labarai na Afirka da kasar Turkiya.
Labarin ya kara da cewa babban daraktan kamfanin dillancin labarai na NAN Mr Buki Ponle ne ya sanya hannu a madadin kamfanin, a yayinda Serdar Aragoz shugaban kwamitin gudanarwa da kamafanin Anadolu ya sanya hannu a madadin kamfaninsa.
An kafa Anadolu a shekara 1920 a birnin Ankara babban birnin kasar Turkiya, a yayinsa aka kaf NAN a shekara 1976 sannan ya fara aiki a shekara 1978.
Kamfanonin biyu zasu yi musayan labarai da harshen turanci, bidiyoyi da kuma hotuna a tsakaninsu.
342/