Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

25 Mayu 2022

18:08:07
1260901

​China Ta Gargadi Amurka Kan Tsoma Baki Dangane Da Batun Taiwan

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gargadi Amurka da cewa za ta janyo kanta rigimar da ba za ta iya dauka ba, idan ta ci gaba da bin hanyar da ba ta dace ba kan batun Taiwan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan dai ya zo ne a cikin sharhin da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya yi a taron manema labarai a jiya Talata, kan kalaman shugaban Amurka Joe Biden na baya-bayan nan kan Taiwan.

Wang ya ce, "Amurka na yin iya kokarinta wajen yin wasa da kalmomi bisa ka'idar “dunkulalliyar kasar Sin", "Amma ina so in tunatar da bangaren Amurka cewa, babu wani karfi a kowane bangare na duniya, ciki har da ita kanta Amurka, dazai iya kare masu neman ballewar Taiwan daga dunkulalliyar Sin ".

Ya kara da cewa, Amurka ta karya alkawuran da ta dauka kan batun Taiwan, ta kuma yi fatali da ka'idar "Kasar Sin daya", ta kuma yi ta ruguza alkawuran a asirce da bainar jama'a da goyon bayan ayyukan 'yan aware na Taiwan.

Ya ce, "Idan har Amurka ta ci gaba da bin hanyar da ba ta dace ba, ba wai kawai zai haifar da illar da ba za ta iya wargaza dangantakar Sin da Amurka ba, har ma a karshe za ta sanya Amurka ta shiga cikin wani yanayi da ba za ta iya jure masa ba."

Wang ya jaddada cewa, kasar Sin tana da cikakken kwarin gwiwa, da kwarewa da kuma aniyar dakile ayyukan 'yan aware da ke da nufin samun 'yancin kai na Taiwan, da dagewa wajen hana tsoma baki daga waje, da tsayin daka wajen kare ikon mallakar kasa da cikakken ‘yancinta.

Ya karkare da cewa, “Ina ba Amurka shawara da ta saurari wata shahararriyar tsohuwar waka ta al’ummar kasar Sin da ke cewa, idan aboki ya zo ana gaishe shi da ruwan inabi mai kyau, idan kuma kura ta zo, sai a tarbe ta da bindigar farauta.

342/