Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

24 Mayu 2022

19:44:45
1260594

Jamiyar APC Ta Amince Da Sake Fasalin Jadawalin Zaben Fidda Gwani Na Shekara Ta 2023

Sakataren hulda da jama’a na jamiyar APC Felix Mork ya bayyana cewa kwamitin zartarwa na Jami’iyar ya amince da sake fasalin yanayin jadawalin zabukan fidda gwani na jam’iyar don tunkarar zaben shugaban kasa da gwamnoni da yan majalisar tarayya da na jihohi da za’a yi a shekara ta 2023.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yace a ranar 26 ga watan mayu da muke ciki ne za’a gudanar da zaben fidda gwani na yan majalisar wakilai da na dattawa da sauran mukamai, kana kuma za’a gudanar da taro na musamman na zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa a ranar 29 zuwa 30 ga watan da muke ciki.

Hukumar Zaɓe Ta Ƙasa INEC ta gargaɗi dukkan jam’iyyu cewa ba za a ƙara masu ko da wa’adin kwana ɗaya ba, daga wa’adin rufe karɓar sunayen ‘yan takara wanda Dokar Zaɓe ta Ƙasa ta sanya ba.

Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da kan Masu Zaɓe na hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bada wannan gargaɗin cikin wata sanarwa da ya fitar.

342/