Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

24 Mayu 2022

19:42:42
1260592

Kungiyar ISWAP Mai Ikirarin Jihadi Ta Kashe Mutane 30 A Arewa Maso Gabashin Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa Kungiyar ISWAP mai kokarin kafa kasar Musulunci ya yammacin Afrika ta sanar da kashe mutane 30 a matsayin daukar fansa kashe kwamandodinta da dakarun sojin Najeriya suka yi a wani hari ta sama da suka ka kai musu a Arewa masu gabashin jihar Borno.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Majiyar labaran gwamnati ta bayyana cewa yan kungiyar ISWAP sun kai harin ne a yau Talata a kauyen Mudu da ke jihar Borno a iyakarta da kasar Chadi, sai dai ana fuskantar matsalar rashin kyan hanyoyin sadarwa bayan da dakarun kungiyar masu ikirarin Jihadi sun tarwatsa dukkan wayoyi da Naurorin sadarwa dake yankin.

Idan ana ita tunawa a yan makwannin baya -bayan na dakarun soji Nageriya sun kai hari ta sama kan ‘ya’yan kungiyar ta ISwap da abokan hamayyarsu Boko haram tare da kashe wasu manyan kwamandojinsu,

Ita dai kungiyar ISWAP ta fice daga Boko haram ne a shekara ta 2016 yanzu kuma tana kokarin ganin ta sama kungiyar jihadi mafi karfi a yankin. Sai dai dukkan kungiyoyin biyu sun kara tsananta kai hare-haren kan fararen hula da manoma da makiyaya da suke zargin su da yin leken Asiri a kan su.

342/