Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

24 Mayu 2022

19:40:36
1260590

IRGC : Iran Za Ta Dauki Fansa Mai Tsanani Akan Kisan Kanar Dinta

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran, ya yi gargadin cewa Iran za ta dauki fansa mai tsanani kan wadanda suka kashe wani kanar din sojinta a Tehran ranar Lahadi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - "ko shakka babu za mu sa makiya su yi nadama" inji, Manjo Janar Hossein Salami, babban kwamandan dakarun na IRGC.

Wasu ne kan babur suka bindiga Kanar Hassan Sayyad Khodaei, a ranar Lahadi, yana gaf da shiga gidansa a gabashin birnin Tehran.

Kafin hakan dama shugaban kasar ta Iran, Ibrahim Ra’asi, ya bayyan cewa ba wata makawa Iran za ta mayar da martaki kan kisan kanar din na ta.

342/