Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Parstoday
Talata

24 Mayu 2022

19:39:23
1260589

​ MDD Ta Bukaci A Sake Dawo Da Tsarin Zabe A Kasar Libiya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi kira da a sake dawo da tsarin zabe a Libya, wanda aka katse a watan Disamban bara.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mista Guteress ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki wajen shirya zaben na Libiya, dasu dawo kan tsarin zaben cikin gaggawa.

Ya kuma bukace su dasu kaucewa duk wani abu da zai haifar da rarrabuwar kai a kasar.

Sama da masu jefa kuri'a miliyan 2.8 ne suka yi niyyar kada kuri'a a ranar 24 ga Disamba, 2021, saidai basu samu wannan dama ta zaben wanda zai shugabance su.

A bangaren tattalin arziki kuwa, MDD, ta nemi a kaucewa duk abunda zai kawo cikas ko tsaiko wajen fitar da albarkatun man fetur wanda kasar ta dogara da shi domin ci gaba da biyan albashin ma’aikata akan kari.

Libiya, dai ta fada cikin rudani ne tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar mirigayi Mu’ammar Ghaddafi a cikin shekarar 2011, kuma tun lokacin ne take fama da rikici na shugabanci.

342/