Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

24 Mayu 2022

19:36:41
1260587

Iran Da Oman Sun Cimma Yarjeniyoyi Da Dama A Tsakaninsu

Kasashen Iran da Oman sun rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyin hadin gwiwa guda 12 domin kyautata alakar dake a tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Bangarorin sun cimma wannan ne a ziyarar aiki ta yini guda da shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi ya kai a birnin Muscat.

An rattaba hannu kan yarjeniyoyin ne na hadin gwiwa a fannonin makamashi, siyasa, sufuri, alakar diflomasiyya, kasuwanci da tattalin arziki, kimiyya, muhalli da wasannin motsa jiki.

Ministocin harkokin waje, da na masana'antu, ma'adinai da ciniki, da man fetur, da hanyoyi da raya birane da kuma shugaban kungiyar bunkasa kasuwanci ta Iran ne da takwarorinsu na kasar Oman suka sanya hannu kan takardun wadannan yarjeniyoyin.

Iran da masarautar Oman dai na alaka ta kut-da-kut, kuma an bayyana kasuwancin da ke tsakaninsu ya kusan ninkawa sau uku a cikin shekara guda, wanda ya kai na dala biliyan 1,3.

342/