Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Litinin

23 Mayu 2022

16:43:44
1260182

Shahadar Daya Daga Cikin Masu Kare Haramin A Wani Harin Ta'addanci Da Aka Kai A Birnin Tehran

Mai kare haramin "Karnel Sayad Khodaei" ya kasance abun nufin da yan ta'addan wanda suke adawa kan juyin juya hali da suke da alaka da Masu girman kai na duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo rahoton cewa, cibiyar hulda da jama'ai ta IRGC ta sanar da shahadar daya daga cikin masu kare haramin da wasu masu aikata laifin ta’addanci na wasu da ke da alaka da girman kan duniya.

A cikin rahoton yazo cewa, ma'aikatar hulda da jami'ai ta IRGC ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta sanar da ayyukan ta'addanci da ake yiwa juyin juya halin Musulunci da alakar hakan da masu girman kan duniya a cikin shahadar daya daga cikin ma'abota girma da ke kare harami: A yammacin yau (Lahadi) a daya daga cikin lungunan da ke kan titin Mojahedin Islam da ke gabacin Tehran, mai kare haramin "Karnel Sayad Khodaei" ya hadu da 'yan ta'adda masu adawa da juyin juya hali da ke da alaka da girman kan duniya.

Da yake taya jaje da ta'aziyyar shahadar mai girma mai kare haramin "Karnel Sayad Khodaei", wannan sanarwar ta jaddada wa iyalansa cewa: Ana dauki matakin da ya dace don gano tare da kama maharin ko maharan.

342/