Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

20 Mayu 2022

19:08:17
1259232

​Najeriya: Shugaba Muhammadu Buhari Ya Isa Qatar Dun Ta’aziya Da Taya Samun Sarki Murna

Shugaba muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya ya isa kasar Qatar don taya gwamnatin kasar juyayin mustuwar sarki Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan wanda ya rasu a cikin yan kwanakin da suka gabata, sannan da taya sabon sarkin Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan .

Jaridar Premiun times ta Najeriya ta nakalto Garba Shehu mai bawa shugaban kasar shawara kan al-amuran yada labarai yana fadar haka ajiya Alhamis.

Shehu ya kara da cewa shugaban karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu, musamman a bangaren bankado kudaden da yan ta’adda suke amfani da su don ayyukansu a tarayyar Najeriya.

Shugaban ya sami rakiyar wasu daga cikin ministocinsa wadanda sukam hada da karamin ministan harkokin waje Zubairu Dada, ministan sadarwa Isa Fantami, Ministan Abuja Muhammad Bello da kuma ministan zirga-zirgan jiragen sama Hadi Sirika. Ana saran shugaban zai komagida a gobe Asabar.

342/