Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fitar, ta tabbatar da cewa, Lavrov da Abdollahian, a yayin tattaunawar da ta gudana a tsakaninsu a yau Alhamis, bisa shawarar da bangaren Iran ya gabatar, sun mayar da hankali ne kan muhimman batutuwan da suka shafi huldar kasashen biyu, da kuma yadda za a cimma matsaya.
Baya ga haka kuma, da komawa ga aiwatar da cikakken shirin hadin gwiwa kan shirin nukiliyar Iran ta 2015 tsakanin Tehran da gungun P5+1.
Ministocin biyu sun kuma yi musayar ra'ayi, a cewar sanarwar ta Rasha, kan wasu batutuwan gaggawa na yankin da kuma na kasa da kasa, ciki har da sabbin abubuwan da suka faru a halin da ake ciki a Ukraine, inda Moscow ke ci gaba da aikin soja.
342/