Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

19 Mayu 2022

18:46:34
1259028

Kasashe Masu Hako Man Fetur A Afrika Na Gudanar Da Taro A Angola Kan Batun Sanya Hannun Jari

Rahotanni sun bayyana Cewa manyan kasashen masu hakomanfetur a nahiyar Afrika na gudanar da wani taron a birnin Luanda na kasar Angola domin gano bakin zaren hanyoyin da za’a bi wajen samar da wadan zasu zuba hannun jari a bangaren manfetur da makamashi a nahiyar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ana sa bangaren sakatare - janar na kungiyar masu hako man fetur a nahiyar Afrika Umar Ibrahim ya fadi cewa abubuwa da dama sun faru a duniya a yau da suka tabbatar da cewa ba da gaske ake ba game da batun musayar makamashi, domin lokacin da aka zo batun tsaron kasa to sai batun makashin ya shiga cikin barazana, kuma su manta da duk wani batun muyasa, sai su koma suna neman manfetur da iskar Gas da kuma Kwal

Yace karacin masu sanya hannun jari a bangaren manfetur da iskar gas a nahiyar Afrika na tsawon shekaru ya sanya an samu koma baya a yawan adadin man da suke hakowa, takunkumin da aka sanya kan makamashin Rasha ya sa kungiyar OPEC da kawayenta sun tsara yadda za su cimma kaso mafi yawa na manda take fitarwa a kasuwar Duniya

kiddidigar da kungiyar kasashen masu fitar da manfetur ta duniya OPEC ta fiyar ya nuna cewa A watan maris kasahen Angola da Najeriya sun kusan cike rabin gibin da aka samu na yawan man da ake fitarwa a kasuwar mai ta duniya.

342/