Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A lokacin ganawar tasu ministan waje na iran ya mayar da hankali sosai game da muhimmancin karfafa dangantakar dake tsakaninsu da kuma yin aiki da yarjejeniyoyin da aka cimma matsaya a kai, don haka za’a aike da tawagar Iran zuwa kasar Ghana domin fitar da taswirar tsarin dangantaka tsakanin kasashen biyu
Da yake tsokaci game da irin damar da iran take da shi a bangaroyin lafiya ,Noma, masana’antu, Ilimi, kimiya da fasaha da ayyukan injiniya da fada da Taa’danci da tsattsauran ra’ayi ministan ya nuna shirin kasarsa na yin aiki tare da kasar Ghana a dukkan wadannan bangarorin.
Anasa bangaren Mohammad Awal yayi ishara game da muhimmancin kara karfafa dangantaka tsakanin kasashen a bangaren sufurin jirgin ruwa da na sama, da kuma samar da layi jirgin sama kai tsaye zuwa kasar Ghana domin bunkasa harkokin yawon bude ido, masana’antu musamman yawon bude Ido na neman lafiya.
342/