Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

18 Mayu 2022

19:23:52
1258752

Yakin Ukrain: Birnin Mariupol Ya Fada Karkashin Ikon Rasha

Wata majiyar sojojin Ukrain ta bada sanarwan cewa ikon birnin Mariupol ya fada hannun sojojin Rasha, sannan a halin yanzu suna kokarin ganin an ceto rayukan sauran sojojin kasar wadanda suka boye a kamfanin sarrafa karafa na Azovstal.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa sojoji 264 daga ciki har da wadanda suka rauni guda 53 suka bar mabuyarsu a kamfanin.

Labarin ya kara da cewa a halin yanzu ana kokarin ceto rayukan sauran sojojin da suka rage a cikin kamfanin karafan na Azovstal

Haka ma labaran da suke fitowa daga bangaren gwamnatin Rasha ta bayyana cewa sojojin Ukrain 256 suka yin saransa suka kuma aje makamansu, daga cikinsu akwai mutane 51 da suka ji rauni.

Kwanaki 82 cur wadanda sojojin Ukrain suna kokarin hana wannan birnin fadawa hannun sojojin Rasha amma daga karshe sun kasa.

Shugaban Zelesky ya yabawa sojojin da suka ajiye makamansu, ya kuma ce sun yi abinda ya zama wajibi a kansu.

342/