Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

17 Mayu 2022

19:35:31
1258439

​Mali: Sojoji Masu Mulki Sun Sanar da Dakile Wani Yunkurin Juyin Mulki

Gwamnatin Sojin kasar Mali ta sanar da cewar ta murkushe wani yunkurin juyin mulkin da wasu hafsoshin sojoji suka yi da taimakon wata kasar Yammacin duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wata sanarwar da gwamnatin sojin ta karanta ta kafar talabijin din kasar tace wata kungiyar bata garin hafsoshin sojoji da jami’an su tayi yunkurin juyin mulki a daren 11 zuwa 12 ga watan Mayu na wannan shekara ta 2022 amma kuma ba suyi nasara ba .

Sanarwar tace sojojin na samun goyan bayan wata kasar Yammacin duniya ne, amma kuma tace ta murkushe yunkurin ta amfani da kwararrun sojojin ta da sauran jami’an tsaron kasa.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace sanarwar bata yi Karin haske akan assalin abinda ya faru ba, amma kuma ta bayyana kama sojojin da kuma shirin mika su a gaban shari’a ba tare da bayyana sunayen su ba.

Wata majiyar soji ta sanar da kama mutane 10, yayin da gwamnati tace ana ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin domin gano sauran wadanda suke da hannu a yunkurin.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace babu wata alama dake nuna yunkurin a makon jiya har sai lokacin da aka gabatar da sanarwar jiya litinin.

Kasar Mali ta gamu da juyin mulkin sau 2 tun daga watan Agustan shekarar 2020 lokacin da sojoji suka kawar da gwamnatin zababben shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita.

Kasar ta kwashe shekaru tana yaki da mayakan dake ikrarin jihadi dake kuma alaka da kungiyar Al Qaeda da IS, rikicin da ya bazu zuwa kasashen Nijar da Burkina Faso dake makotaka da ita.

Sojojin dake mulki a kasar sun katse hulda da kasar Faransa da ta yiwa Mali mulkin mallaka, yayin da suka rungumi Rasha wajen yaki da Yan ta’adda.

342/