Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

17 Mayu 2022

19:34:49
1258438

​Najeriya: Wani Abu Da Ya Fashe A Unguwar Sabon Gari Kano Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Jama’a

Rahotanni daga jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya na cewa wani abu ya tashi a Aba Road da ke Unguwar Sabon Gari a birnin Kanon.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a wata makarantar yara ta Winner Kids Academy, kuma abin ya rutsa har da wasu yara daga cikin ‘yan makarantar

Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano CP Sama'ila Dikko da shugaban hukumar DSS na jihar Kano da wasu daga cikin amnyan jami’an tsaro sun halarci wajen da abin ya faru, sannan motocin asibiti sun je don kwasar waɗanda harin ya rutsa da su a wurin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa abin da ya fashe wanda ake zaton bam ne, tabbas ya yi sanadin asarar rayuka da kuma jikkatar wasu mutanen, duk kuwa da cewa har yanzu ana matakin bincike domin sanin hakikanin abin da ya faru.

342/