Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Iran ya nakalto kamfanin dillancin labaran kasar Qatar (QNA) yana fadar haka ya kumakara da cewa Mohammad bin Abdul Rahman Al Thani da Antony Blinken sun tattauna dangane da yaki a Ukrain, Afganistan da kuma dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Wannan tattaunawar dai tana zuwa ne kwanaki bayan da sarkin kasar Qatar ya kawo ziyarar aiki a nan Tehran. Har’ila yau kafin haka Mohammad bin Abdul Rahman Al Thani ya tattauna da jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na kasar Kasar Josept Borrell da kuma Robert Mali jami’a mai kula da al’amuran kasar Iran na gwamnatin shugaban Biden kan batun.
342/