Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

16 Mayu 2022

15:33:03
1258146

Iran, Pakistan Da China Sun Gudanar Da Taron Kawance Na Majalisun Dokokinsu

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hussain Amir Abdullhiyan ya halarci taron kwancen majalisun dokokin kasashen Iran, Pakistan da kuma China a nan birnin Tehran a jiya Lahadi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran yana fada a cikin taronnjan cewa karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu yana da muhimmanci, don irin matsayin da suke da shi a yankin don kuma kare mutanen kasashensu.

Daga karshe ministan ya bayyana cewa Iran tana son ganin an aiwatar da yarjejeniyar mai muhimmaci wacce Iran da cimma da kasar rasha a cikin yan shekarun da suka gabata.

342/