Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

15 Mayu 2022

16:33:33
1257825

​Iran: A Shirye Muke Domin Cimma Matsaya A Tattaunawar Vienna

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bagheri Kani, babban mai shiga tsakani na kasar Iran ya tabbatar da cewa, duk da irin muhimmancin da Iran ta baiwa tattaunawar Vienna da kuma tsayawa kai da fata a kan manufofinta, a lokaci guda kuma ba za ta taba amincewa da makiyanta ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da Bagheri Kani ya fitar a safiyar yau Lahadi, a ziyarar gani da ido day a kai a wajen baje kolin kayan man fetur da iskar gas na kasa da kasa, inda ya ce: hanyoyin da ake bi domin janye takunkumin ana yin taka tsantsan a kansu, domin kaucewa wani makircin wanda za a iya yin amfani da shi domin cutar da Iran ta wani bangaren.

Da yake magana game da soke takunkumin, ya ce: manajoji da ƙwararrun masana'antar makamashi a ƙasar sun canza salon hanyoyin dage takunkumin," wanda kuma a lokaci guda yana da alaka da sauran hanyoyin na farko, domin tabbatar da cewa Amurka ba ta sake samun damar yin wata kutunguila a kan lamarin ba.

Bagheri Kani ya jaddada cewa, tsayin aka da kasarsa ta yi, shi ne ya yi tasiri wajen sanya sauran bangarorin da suke cikin yarjejeniyar daukar batun da muhimmanci, domin kuwa idan ba a cimma matsaya ba, Iran tana da wasu matakai na gaba da za ta dauka a cikin shirin nata na nukiliya.

<p "="">A cikins hekara ta 2015 ce aka cimma yarjejeniya kan shirin Iran na nukiliya tsakaninta da manyan kasashen duniya, amma a cikin shekara ta 2018, shugaban Amurka na lokacin Donald Trump ya fitar da kasar daga cikin wannan yarjejeniyar, lamarin da ya sanya Iran ta dauki matakin yin watsi da wasu bangarorin yarjejeniyar daga na bangaren, bayan da sauran kasashen turai suka kasa cika alkawullan ad suka dauka bayan ficewar Amurka.

342/