Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

15 Mayu 2022

16:26:28
1257817

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jamio’I A Najeriya Ta Sanar Da Sakamakon Jarabawar Ta Bana

Kakkakin hukumar shirya jarabawar shiga jami’oi a Najeriya JAMB Dr Fabian Benjamin shi ne ya fitar da sanarwar a jiya Asabar ta sakin sakamakon jarbawar da aka yi a wannan shekarar ta 2022 , inda aka bukaci dukkan wadanda suka zana jarabawar da su yi amfani da lambar layin wayar da suka yi rijister sunayensu domin duba sakamakon jarabawar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yace wannan ita ce hanyar da aza’a bi wajen doba sakamakon jarabawar saboda har yanzu hukumar bata wallafa sakamakon a shafinta ba saboda da wasu dalilai da bat a bayyana ba.

Bugu da kari an yi gargadi cewa daliban za su rika samun sakonni iri daban daban daga yan damfara kan yadda za su duba sakamakonsu sabanin wanda aka sanar, don haka an bukaci das u watsi da duk irin wadannan sakonni domin dukkansu hanyoyin ne na yaudara .

An gudanar da jarabawar neman shiga jami’oi ne a ranar juma’a 6 ga watan mayun shekara ta 2022 kuma aka kammala a ranar juma’a 13 ga watan na mayun shekara ta 2022

342/