Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

8 Mayu 2022

15:10:41
1255813

Enrique Mora, Zai Ziyarci Iran, Game Da Batun Tattaunawar Vienna

Kungiyar tarayyar turai ta ce mukadashin babban jami'inta mai kula da harkokin waje turai Enrique Mora zai ziyarci birnin Tehran inda zai gana da babban mai shiga tsakani na Iran a tattaunawar Vienna Ali Bagheri Kani.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ziyarar na da manufar tattauna batutuwan da suka rage masu tsarkakakiya game da tattaunawar Vienna da ta shiga rashin tabbas.

Mista Mora, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin hadin gwiwa na yarjejeniyar nukiliya, zai iso ne Tehran a ranar Talata mai zuwa domin tattaunawa da manyan jami'an kasar Iran kan muhimman batutuwan da suka shafi farfado da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran a 2015.

Tattaunawar Vienna da aka kwashe tsawon lokaci ana yi ta shiga halin rashin tabass ne tun bayan da Amurka ta ce ita fa ba za ta janye takunkumin da ta kakabawa dakarun kare juyin juya halin musulinci na Iran ba, wanda kuma daya ne daga cikin sharuddan da gwamnatin Tehran ta gabatar.

342/