Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Hakan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da kamfanonin jiragen suka bayyana shirin dakatar da ayyukansu daga ranar Litinin 9 ga watan Mayun 2022, saboda tsadar man jiragen da ya tashi daga Naira 190 kan kowace lita zuwa Naira 700, ya haifar da matsaloli masu yawa ga kamfanonin jiragen.
Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin jama’a ga ministan sufurin jiragen sama, James Odaudu, ya fitar a ranar Asabar, inda ministan ya bukaci kamfanonin jiragen sama da su yi la’akari da illolin da matakin zai haifar, tare da nuna damuwarsa kan karuwar farashin man jirgin sama.
342/