Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

8 Mayu 2022

15:04:44
1255808

​Rasha Ta Sanar Da Ragargaza Wasu Tarin Makamai Da Kasashen Turai Suka Aike Zuwa Ukraine

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da ragargaza wasu makamai masu linzami na Amurka da na yammacin Turai a yankin Kharkov da ke gabashin kasar Ukraine, inda rundunar sojin ta Rasha ta yi amfani da makamin "Iskander" mai linzami wajen kai harin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Rasha Igor Konashenkov ne ya bayyana hakan a yammacin jiya Asabar, inda ya ce sojojin kasar Rasha sun ragargaza makamai masu linzami a kusa da tashoshin jiragen kasa na Krasnograd da Karlovka na lardin Kharkov.

Ya ce daga ciki akwai makamai masu tarin yawa da kayan aikin soja, wadanda suka isa wurin, wadanda suka fito daga Amurka da kasashen Yammacin turai domin yaki da Rasha.

Haka nan kuma sojojin na Rasha sun kwace iko barikicin sojojin Ukraine na bataliyar sojojin ta 58 ta Ukrainian Mechanized Infantry Brigade da ke yankin.

Moscow ta yi gargadin fiye da sau tari kan cewa duk wasu makaman NATO da suka isa Ukraine, to za ta ragargaza su.

342/