Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Bawa ya kara da cewa hukumarsa zata bi duddugin dukkan kudaden ‘yan siyasa suke kashewa don hawa kan kujerun shugabanci daban daban a kasar, daga ciki har da kudaden sayan fom na takarar zabe daga na majalisar wakilai da har zuwa shugaban kasa.
Kafin haka dai yawan kudaden sayan fom na shiga takarar shugaban kasa, musamman a jam’iyya mai mulki APC da kuma PDP babban jam’iyyar adawa ya jawo korafe-korafe da dama a cikin mutanen kasar.
Labarin ya kara da cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta sanya Naira miliyon 100 a matsayin farashin sayan fom don shiga takarar shugabancin kasa, sannan PDP kuma ta sanya naira miliyon 40 don sayan fom kawai. Daga karshe bawa ya kammala da cewa suna sun hana gurbatattun yan siyasa rike mukamai a kasar.
342/