Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

7 Mayu 2022

19:07:20
1255503

​Ukrain: Sabbin Labarai Kwanaki 73 Da Fara Yaki Na Musamman A Kasar Ukrain

Kwanaki 73 kenan da fara yaki a kasar Ukrai, ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta bayyana cewa ta lala makaman kakkabo jiragen sama 300 a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - na kasar Siriya ya nakalto ma’aikatar na cewa sojojin Rasha sun wargaza makamai da dama wadanda aka shigo da su kasar ta Ukrain daga Amurka da kasashen Turai a yankin Kharkiv.

Banda haka labarin ya kara da cewa sojojin Rasha sun wargaza sansanonin sojojin Ukrain 44 a daren jiya Jumma’a a yankin Dones wanda ya balle daga kasar Ukrain ya kuma nemi taimakon gwamnatin Rasha don kare ta daga gwamnatin Ukrain.

342/