Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A shekara ta 2020 kasar Armeniya ta gwabza fada da jamhuriayr Azarbaijan a karo na biyu kan hakkin ikon mallakar Nagorno- Karabakh sai dai an kawo karshen yakin bayan kwanaki 44 bayan da kasar rasha ta shiga tsakanin inda aka rattaba hannun kan yarjejeniyoyi guda 3 da ake kira da tripartite
A daren jiya ne kasar Azarbaijan ta sanar cewa an kai hark an sansanin sojojinta dake iyakar tad a Armeniya shi ma a nasa bangaren ministan tsaron kasar Armeniya ya fadi cewa sojojin Azarbaijan suk kai hari kan sansanin sojojinta da gangan, a garin Zilki dake yankin Kalbajar, da suka yi amfani da kananan makamai , sai dai tuni dakarunsu suka mayar da martani, amma babu Karin haske game da wadanda suka rasa rayukansu ko kuma suka jikkata ko asarar dukiyoyi
Jamiyun adawa a kasar ta Aremeniya sun zargi fira ministan kasar Nikol Pashinyan da kokarin mika yankin na Nagorno –Karabakh ga kasar Azarbaijan..
342/