Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

4 Mayu 2022

18:56:11
1254551

Sakataren M D D, Guterres, Ya Isa Borno Kuma Ya Yaba Da Mataken Da Gwamnatin Ke Dauka

Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, Ya isa jihar Borno ne da ke arewa maso gabashin Nijeriya a jiya Talata da yamma, , domin duba halin da yankin ke ciki sakamakon rikicin Boko Haram da aka kwashe shekaru ana yi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ne ya tarbe Guterres a lokacin da ya isa filin jirgin sama na Maiduguri. A ganawar da suka yi da gwamnan jihar ya jinjina masa game kokarin da yake yin a fada day an ta’adda kuma ya goyi bayan tsarin gyaran hali day a bullo das hi ga tubabbun boko Haram a suka ajiye makamansu suka rungumi zaman lafiya, kuma ya bayyana hakan a matsayin Mabudin samar da zaman lafiya a kasa mafi yawan jama’a a Afrika

Nageriya ta kwashe fiye da shekaru 10 tan ayaki da mayakan kungiyar Boko Harram dana Iswap masu ikirarin kafa gwamnatin Musulunci a yammacin Afrika, da hakan yayi sanadiyar mutuwar Dubban mutane Da Kuma Tilastawa miliyoyi barin gidajensu ba shiri.

Ana sa bangaren gwamnatin jihar Borno Zukum ya fadi cewa akalla akwai mayakan boko haram da iyalansu guda 40,000 da suka mika wuya ga gwamnati tun daga shekarar da ta gabata, tun bayan kashe shugabansu a farkon shekara ta 2021,

Daga karshe Gutteres ya ziyardi sansanin yan gudun hijira da gidajen wasu yan boko Haram din suka tuba suka ajiye makamansu, da yake ganawa da manema labarai ya ce batun gyara halayenwadanda suka ajiye makamansu domin fara wata sabuwar rayuwa zai taimaka sosai wajen cimma zaman lafiya.

342/