Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

30 Afirilu 2022

19:20:50
1253504

​Lavrov: Rasha Ba Ta Yi Wa Kowa Barazana Da Makaman Nukiliya

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce Rasha ba ta yi wa kowa barazana da yakin nukiliya, yana mai cewa Ukraine da Poland ne ke furta munanan kalamai a kan haka.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Lavrov ya fada a cikin wata sanarwa da ya aikewa tashar Al-Arabiya cewa: "Sun tambaye ni ko yakin nukiliya na iya yiwuwa, ko hadarin makaman nukiliya ya karu kuma ko Rasha ta yi imanin cewa hakan zai yiwu?

Na maimaita cewa tun farkon hadin gwiwarmu da Gwamnatin Trump muna ba da shawarar sake tabbatar da sanarwar Reagan, Kuma Gorbachev daga 1987 ya yi nanata cewa ba za a iya samun nasara a yaƙin nukiliya ba, don haka bai kamata a yi shi ba."

Lavrov ya kara da cewa, "Ba mu wasa da batun yakin nukiliya, yayin da yake magana kan kalaman shugaban kasar Ukraine Vladimir Zelensky na cewa "Ukrain ta yi kuskure a lokacin da ta yi watsi da matsayinta na nukiliya, da kuma cewa za ta sake tunani game da mallakar makaman nukiliya."

Ya kara da cewa, ya kamata kasashen Yamma su matsa lamba kan abokan huldar su, saboda "Ukraine da Poland ba sa kaurace wa kalamai masu hadari."

Ya kara da cewa, siyasar kasashen turai da NATO su ne suka jawo rikicin kasar Ikraine, yayin da kuma abin takaici Ukraine ta biye musu ta zama ‘yar amshin shata da ake amfani da ita domin cutar da Rasha.

342/