Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

26 Afirilu 2022

19:08:19
1252060

​Fiye Da Mutane Saba’in Aka Kashe A Wani fadan Kabilanci A Sudan Ta Kudu

Akalla fararen hula saba’in da biyu ne aka kashe cikin makwanni bakwai a Sudan ta Kudu, tare da yanke kawunan wasu da kona wasu da ransu, yayin da rikicin kabilanci ya barke a yankin da ke da arzikin man fetur.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Gidan Rediyon faransa ya bayar da rahoton cewa, Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta kudu ya ce, rahotanni sun nuna cewa zubar da jinin da aka yi tsakanin 17 ga watan Fabrairu zuwa 7 ga Afrilu a gundumar Leer da ke jihar Unity ya tilastawa mutane 40,000 tserewa daga gidajensu, inda masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya suka ce an samu rahotannin laifuka 64 na cin zarafin mata.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, wasu mata biyu sun shaida wa tawagar Majalisar Dinkin Duniya cewa gungun wasu matasa masu dauke da makamai sunyi musu fyade sau da dama a lokacin da suka fito daga maboyar su domin nemawa ‘ya’yan su abinci.

Wata mata da ta haihu a kwanan nan ta ce itama ta fuskanci irin wannan al’amari sannan kuma an yi ta dukan ta har na tsawon kwanaki uku.

Rikicin dai ya haifar da fargabar a kasar da ta sha fama da yakin basasa, bayan shekaru biyu da samun 'yancin kai daga Sudan.

Fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun da ke biyayya ga shugaba Salva Kiir da kuma na mataimakinsa Riek Machar ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 400,000 kafin bangarorin biyu su amince su ajiye makamai a shekarar 2018.

Sai dai kasar mai mutane miliyan 11 ta yi kokarin dawo da dauwa mammen zaman lafiya a cikin shekaru masu zuwa, duk da fama da rashin bin doka da tashe-tsahen hankula da ke da nasaba da rikicin kabilanci.

342/