Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

26 Afirilu 2022

19:05:08
1252057

Ukraine : Rasha Ta Ce Akwai Hadarin Shiga Yakin Duniya Na Uku

Kasar Rasha, ta bayyana cewa, baiwa kasar Ukraine makamai da kasashen yamma ke yi tamkar kungiyar Nato ta shiga yaki da Rasha ne.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministan harkokin wajen Rashar ne Sergueï Lavrov, ya bayyana hakan, yana mai gargadi akan hadarin dake tattare da hakan wanda kan iya haifar da yakin duniya na uku.

A cewarsa Nato, ta shiga yaki da Rasha, ta wata hanya, kuma tana mikawa wadannan makamai, wanda yana nufin ta shiga yakin.

Wannan dai na zuwa ne bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka da kuma na tsaronta suka kai a birnin Kiev, inda sukayi alkawarin taimakawa Ukraine da karin makaman yaki.

Mista Lavrov, ya kuma ce, sojojin Rasha zasu dauki mataki kan duk irin wadanan makamman.

342/