Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

26 Afirilu 2022

19:00:23
1252056

Burkina Faso, Ta Yi Biris Da Wa’adin ECOWAS, Na Shirya Zabe

Sojojin dake rike da mulki a Burkina faso, sun yi biris da wa’adin da kungiyar ECOWAS, ta dibar musu na su fitar da jadawalin shirya zabe domin mika milki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ranar 25 ga watan Afrilu ne wa’adin da ECOWAS, din ta dibarwa sojojin domin gabatar da jadawalin shirya zabe, saidai kakakin gwamnatin Burkina faso, ya bayyanawa kamfanin dilancin labaren AFP, cewa babu wani sabon jadawali da zasu gabatar na rikon kwarya.

Lionel Bilgo, ya ce ba zasuyi watsi da shirin shinfida zaman lafiya a kasar ba, su maida hankali kan shirya jadawalin zabe ba.

Sojojin na Burkina faso, dai sun ce suna bukatar wa’adin shekara uku kafin su gudanar da zabe, wanda kuma kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrikar ke cewa ya yi yawa sosai,

Ecowas, dai ta yi barazar kakabawa Burkina fason takunkumi tattalin arziki, koda yake kungiyar bata ce uffan ba kawo yanzu kan batun.

342/