Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

25 Afirilu 2022

17:36:00
1251665

Putin Ya Taya Macron Murnar Sake Lashe Zaben Shugaban Faransa

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya aikewa da takwaransa na faransa Emanuel Macron sakon taya murna game da sake lashe zaben shugaban kasar, duk da sabanin dake tsakanin kasashen game da yakin Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A sakon da fadar Kremlin ta fitar Mista Putin, ya ce yana taya Macron murna tare da yi masa fatan samun ci gaba a ayyukansa, da kuma fatan koshin lafiya a wa’adin mulkinsa na biyu.

Kafin shugaban kasar ta Rasha, shugabannin kasashen duniya da dama musamman ma na turai sun taya zababen shugaban kasar ta faransa murna game da nasarar lashe zaben.

Shugaba Macron dai mai ra’ayin tsaka-tsaki ya kayar da abokiyar hamayarsa mai ra’ayin rikau Marine Le Pen da kashi sama da 58 %, na yawan kuri’un da aka kada a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a jiya Lahadi, yayin da ita kuwa Madame Le Pen ta samu kashi sama 41 cikin dari.

342/