Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

25 Afirilu 2022

17:35:10
1251664

Sudan : Mutum 160 Sun Mutu A Wani Rikicin Kabilanci A Darfour

Bayanai daga Sudan, an cewa akalla mutane 160 ne suka mutu a wasu rikice-rikice masu nasaba da kabilanci a yankin Darfour.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rahotannin sun ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi, a yankin dake yammacin kasar da ya jima yana fama da yakin basasa, kamar yadda kakain hukumar kula da ‘yan gudun hijira a yankin na Darfour ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP.

Rikicin a cewar bayannai ya fara ne ranar Juma’a a inda aka kashe mutum takwas a yankin Krink, dake nisan kilomita 80 daga Lardin El-Geneina, babban birnin yammacin Darfour.
Wasu mas dauke da makamai ‘yan kabilar larabawan Rzeigat, suka farmawa kauyen ‘yan kabilar nan ta Afrika Massalit, a mastayin maida martani kan wasu mambobinta biyu.

342/