Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

24 Afirilu 2022

16:46:20
1251337

Faransa : Le Pen Da Macron Na Fafatawa A Zaben Shugaban Kasa

A Faransa yau Lahadi ne ‘yan takaran da suke wuce a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Marine Le Pen da Emanuel Macron ke fafatawa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan shi ne karo na biyu da Shugaba Macron mai ra’ayin tsaka-tsaki ke fafatwa da madame Le Pen mai ra’ayin rikau a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar bayan na 2017, da ya bashi damar darewa kan karagar mulkin kasar.

Sakamakon jin ra’ayin jama’a ya nuna cewa shugaban mai barin gado zai iya lashe zaben da kashi 54 zuwa 56,5 cikin dari, yayin da ita kuwa Le Pen kan iya samun kashi 43,5 zuwa 46 cikin dari.

Saidai akwai fargaba game da fitowar jama’a yayin kada kuri'a a zaben na yau.

342/