Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Asabar

23 Afirilu 2022

18:40:29
1250943

Bayanin Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya Bayan Sabbin Hare-haren Ta'addanci Da Aka Kai A Yammacin Kabul

Majalisar Malaman Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya ta fitar da bayanin tir dangane da sabbin hare-haren ta'addanci da aka kai a yammacin Kabul.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo rahoton cewa, Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya ta fitar da wata sanarwa dangane da sabbin hare-haren ta'addanci da aka kai a yammacin birnin Kabul.

Bayanin na Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya ya zo kamar haka;

Da sunan Ubangijin shahidai da salihai

Har yanzu muna jimamin rashin almajirai da dalibai da ‘ya’yan al’ummar musulmi a cikin hare-haren ta’addancin da aka yi a cibiyar “Kabul Tebyan” da “Makarantar Sayyidush Shuhada'a Dasht Barchi” da “Masallatan ‘yan Shi’a a Kunduz da Kandahar”; Wannan zafin da radadin ya sake sabunta.

Makiya Allah da na al’umma kamar watan Ramadan na shekarar da ta gabata, a bana ma sun kai hari a makarantun ‘yan Shi’a da ake zalunta a birnin Kabul, inda suka kashe dimbin jama’a; Kuma har ya zuwa ina za mu iya dauka da jure zafin hakan, wadanda aka yi wa wadannan ta'addancin yara ne da matasa marasa laifi.

Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya a yayin da take nuna juyayi da goyon bayan al'ummar Afganistan - musamman ma iyalan wadanda wannan bala'i ya rutsa da su - suna matukar yin Allah wadai da hakan, tare da yin kira ga Mahukunta da su tabbatar da sun hukunta masu kai irin wadannan hare-hare na dabbanci.

Majalisar ta kuma jaddada bukatar hadin kan 'yan Shi'a da Sunna da dukkan kabilu a kasar Afganistan, tare da yin kira ga mahukuntan kasar da su tabbatar da tsaron wuraren Kimiyya da ilimi da al'adu da na Shi'a kamar yadda aka yi alkawari a baya.

Hare-haren kunar bakin wake da aka yi a watannin da suka gabata - wadanda akasarinsu akan 'yan Shi'a ne - ya nuna cewa gwamnati ba ta da wani tasiri wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arzikin da jama'a ke fama da su, har ma da gazawa wajen tabbatar da su.
Ko shakka babu mahukuntan Afganistan za su iya shawo kan wadannan matsaloli idan sun nemi taimakon malamai da 'yan shi'ar kasar nan don kare al'ummarsu da samar da tsaro a yankunansu.

Ci gaban Afghanistan da sake gina ta ba zai yiwu ba sai da zaman lafiya da tsaro; Kuma za a iya samun tsaro da kwanciyar hankali ne idan aka kafa gwamnati mai cikakken iko bisa amincewar dukkanin kabilu da addinai da ake mulkarsu a kasar.

A karshe babban abin takaicin mu da jajantawarmu na rashin Daliban Makarantun guda biyu ‘Mumtaz’ da ‘Abdul Rahim Shahid’ da aka yi gaban Imam Zaman (AS) da kuma al’ummar musulmi, da al’ummar Afganistan da ke shan wahala da kuma su iyalan Shahidan. Allah ya jikan wadancan shahidan Muna fatan kasancewar wadannan Shahidai tare da waliyyan Allah, muna kuma fatan samun lafiya ga wadanda suka jikkata cikin gaggawa.

"وسيعَلَمُ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَيَ مُنقَلَبٍ يَنقَلِبُون"
Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya

21' Afrilu , 2022