Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Rasha Major General Igor Konashenkov ne ya sanar da cewa; Baya ga lalata makamin da aka bai wa Ukiraniya sun kuma kashe sojojin da suka kai 25 a garin na Dnipro.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai kasar Slovakia ta sanar da aike wa Ukiraniya makamin S-300 wanda kirar Rasha ne, kuma ana amfani da shi ne wajen karbo jiragen sama da makamai masu linzami.
A gefe daya, ma’aikatar tsaron Rasha, ta kuma sanar da cewa sojojin Ukiraniya da suke samun taimakon kasashen turai suna shirin yi wa fararen hula a yankin Logans kisan kiyashi.
Tun a makon da ya wuce ne dai kasar Ukiraniya ta zargi Rash da yi wa fararen hula kisan kiyashi a garin Bucha, da wasu garuruwan da suke zagayen birnin Kiev.
342/