Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Lahadi

10 Afirilu 2022

20:55:02
1246854

Gayyatar Shiga Gasa Karo Na Uku Ta Zanen Kartoon Na Ranar Quds Ta Duniya + Yana Dauke Da Fosta Da Fam Ɗin Yin Rajista

A daidai lokacin da watan Ramadan na shekara ta 1443 bayan hijira da kuma karatowar ranar Qudus ta duniya ake gayyata shiga "bikin zane-zane na duniya karo na uku na ranar Qudus ta duniya".

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya habarta cewa, a daidai lokacin da watan Ramadan na shekara ta 1443 bayan hijira da kuma jajibirin ranar Qudus ta duniya, ake gudanar da bikin zane-zane na ranar Qudus ta duniya karo na uku.

Bikin zanen Cartoon na ranar Qudus ta duniya karo na uku

Wanda aka sanyawa take kamar haka:
"Cin Amana Itace Sila" Da "Ranar Musiba"

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai JinKai

"Ranar Kudus ranar Musulunci ce" Imam Khumaini

"A gaskiya, zane-zanenmu yana taka rawa a cikin harkokin kasa da kasa, kuma dole ne mu gode wa matasa nagari da suke aiki a kai." Imam Khamenei

A daidai lokacin da watan Ramadan na shekara ta 1443 bayan hijira da kuma jajibirin ranar Qudus ta duniya ake kiran "bikin zane-zane na ranar Qudus ta duniya karo na uku".

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA – ta shirya wannan bikin gasar ne tare da hadin gwiwar kwamitin goyon bayan juyin juya halin Musulunci na al’ummar Palastinu (mai alaka da fadar shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran) Cibiyar Nazarin Dabaru ta “Shahid Fazel (Iraq), Kungiyar "Tayyar Al-Wafa" "Islamic (Bahrain)", "Cibiyar Fasahar Juyin Juya Halin Musulunci (Iran)" da " site day tattara fasahar Musulunci".

* Maudu'i:
Yayin da wannan lokaci na bikin ya zo daidai da kokarin da ake yi na girma da jiji da kan kasashe ta hanyar daidaita alaka tsakanin kasashen Larabawa da na Musulunci da gwamnatin mamaya ta Yahudawan Sahyoniya, bisa la’akari da kuma kusantowar ranar shan wahala da ranar Kudus ta bana, duba da haka za’a gudanar da shi ne a wadannan batutuwa guda biyu:

1. Cin amanar wasu shugabannin larabawa wajen daidaita alaka da Isra'ila

2. Ranar Musiba (ranar kafuwar Isra'ila da gudun hijirar al'ummar Palastinu).

* Tsarin Gudanarwa:

1. Kowane mai zane-zane na iya shiga cikin kowane batutuwan gasar tare da matsakaicin ayyuka 3 (cikin batutwan ayyuka guda 6).

2. Girman zane-zanen da za’a ƙaddamar dole ne ya zama A4 a cikin tsarin jpg da tsarin dpi 300.

3. Dabarar gudanarwar kai tsaaya ne babu iyakancwa.

4. Hotunan zanenda za’a aiko dashi dole ne a sanya sunansu da Ingilishi bisa ga misali mai zuwa:

Sunan, da sunan mahaifin mai zane - lambar aiki - lambar wayar hannu (tare da prefix na ƙasa). kamar haka:

Amir, Amiri01-00989120000000.jpg

5. Dole ne a aika da zane-zane ta imel zuwa sakataran bikin a matsayin attached file "haɗedɗen Fayil".

6. Masu shiga dole ne su cika fom ɗin halartar gasar su hada tare hoton su da zane-zanen da su kayi su tura ta Imel.

7. A wajen Hukumar gudanarwar duk wanda ya aiko da fom ɗin shine a matsayin yake da mallakin zanen cartoon ɗin da aka ƙaddamar kuma, idan an tabbatar da sabanin hakan, za ta cire aikinsa daga gasar.

8. kar ya zamo zanennukan Kartoon da aka gabatar an karbi kyautar ta hanyar wasu gasar da aka gabatar a wani gurin. Idan ba kiyaye wannan sharadin ba, ba za a shigar da aikin da aka gabatar a cikin gasar ba kuma za a iya iya karbe kyautar da za aka samu bayan gane hakan.

9. Ayyukan da suka shafi batutuwa biyu da aka anbata asama a tare akansu za a yi hukunci.

10. Hukumar gudanarwar tana da haƙƙin yin amfani da ayyukan yan takarar gasar, ta kowace hanya.

11. Duk mahalarta za a ba su takardar shaidar halartar bikin gasar.

12. Aika zane-zane yana nufin yarda da ka'idojin gasar.

* Kyaututtuka:

Mutum Na Farko: Takardar shedar kwarewa ta girmamawa da kudi Yuro 1500.

Mutum Na Biyu: Takardar shedar kwarewa ta girmamawa da kudi Yuro 1000.

Mutum Na Uku: Takardar shedar kwarewa ta girmamawa da kudi Yuro 700.

* Yadda Za’a Aika Ayyukan:

1. Tazara Lokacin Tura Ayyukan:

Matsakaicin ranar ƙarshe don karɓar zanen zuwa hukumar bikin shine 21 ga Yuni, 2022.

2. Yadda Ake Aikawa:

Dole ne mahalarta su aika da "zanen da sukayi", "fum ɗin da suka cike" da "hotansu" ta imel ɗin bikin ([email protected]).

Danna kan "Download" domin sauke fam ɗin rajistar.


Fom ɗin rajista don bugu na uku na bikin Batun Ranar Quds na Duniya

Download


* Hanyoyin Tuntuɓi Hukumar Gudanarwa:

Idan kuna da wasu sharhi, shawarwari, tambayoyi ko matsaloli wajen ƙaddamar da ayyuka, tuntuɓi hukumar bikin ta hanyoyi masu zuwa:

Lambar waya: 025-32131320 (lokacin kira daga 8 na safe zuwa 2 na rana)

Lambar wayar hannu: 09122530366

Lambar SMS: 30008070900000

Yanar Gizo: https://arts.fa.abna24.com/p/cartoon-quds-1443

Imel: [email protected]

.................................