Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

10 Afirilu 2022

20:33:33
1246841

​Koriya Ta Arewa Ta Caccaki Shugaban Amurka Joe Biden

Koriya ta Arewa ta bayyana shugaban Amurka Joe Biden a matsayin rudadden tsoho, biyo bayan wasu kalamasa na suka ga shugaban Rasha Vladimir Putin na laifukan yaki a Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wani bayani da kamfanin dillancin labaran gwamnatin Koriya ta Arewa ya buga a ranar jiya Asabar, shi ne game da shugaban Amurka wanda ya yi kalaman batunci ga shugaban na Rasha bisa dogaro da wasu bayanai marasa tushe a cewar gwamnatin Koriya ta Arewa.

Bayanin ya kara da cewa "Irin wadannan maganganu na rashin hankali babu wanda zai yi sua duniya sai mutane marasa kan gado da kuma wauta irin ta tsufa.

Bayanin ya bayyana Biden a matsayin mutumin da aka sani da yawan zamewar harshe a lokacin magana, amma ba tare da bayanin ya ambaci sunansa kai tsaye ba.

Gwamnatin kasar Koriya ta Arewa tana goyon bayan kasar kan ayyukan sojin da take gudanarwa a kasar Ukraine, tare da bayyana cewa Amurka da kasashen turai su ne ummul haba’isin dukkanin abin da yake faruwa, ta hanyar yin ingiza mai kantu ruwa da suka yi wa mahukuntan Ukraine, wadanda suka dauka cewa turawa abin dogara ne.

342/