Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

9 Afirilu 2022

15:02:44
1246459

Rasha Ta Kori Amnesty Da Human Rights Watch

Rasha ta sanar da kawo karshen ayyukan wasu kungiyoyin kasa da kasa masu zaman kansu a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Matakin ya shafi kungiyoyi 15 cikinsu har da kungiyoyi masu rajin kare hakkin bil adama na kasa da kasa irinsu Amnesty International ta Biritaniya da Human Rights Watch ta Amurka da kuam wasu na Jamus.

Wata sanarwa da ma’aikatar shari’ar Rashar ta fitar ta ce an dakatar da kungiyoyin saboda take dokokin kasar.

Babbar sakatariyar kungiyar Amnessty, ta maida martani kan matakin na Rasha, tana mai cewa an hukuntasu saboda kare hakkin dan adam da kuam gayawa hukumomin Rasha gaskia.

Agnès Callamard, ta ce kure ne mahukuntan Rasha, sukayi idan suna tsammanin rufe ofishinsu a Moscow zai dakatar da aikinsu.

Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da takaddama tsakanin kasashen yamma da kuma Rashar game da matakin sojin da ta dauka kan Ukraine tun ranar 24 ga watan Fabarairu.

342/