Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministan yada labarai na Rashar, ya tabbatar cewa babu wasu fararen hula da sojojin kasar suka kashe a Boutcha, kuma gawarwakin da ake nunawa yashe cikin titi a garin na Boutcha wani shiri ne na Keiv domin kafafen yada labarai na kasashen yamma.
Ya, ce a tsawon lokacin da sojojin na Rasha, suka kasance a yankin, babu wani farar hula na yankin da aka gallazawa.
Sanarwar da ma’aikatar tsaron Rashar ta fitar ta ce sojojinta sun raba tonne 452 na kayan jin kai ga fararen hula a yankin, kuma duk fararen hula dake a wajen sun samu damar ficewa cikin ‘yanci zuwa yankunan arewaci a daidai lokacin da dakarun Ukraine ke barin wuta ba dare ba rana.
A baya baya nan ne dai akayi ta yada wasu hotunan bidiyo na wasu gawarwarkin mutane 410 yashe a birnin na Boutcha wanda sojojin Rashar suka fice, lamarin da tuni kasashen yamma suka danganka da laifukan yaki idan sun tabbata.
342/