Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

24 Maris 2022

16:59:40
1242088

Shugabannin Yamma Na Taro Kan Ukraine

Shugabannin kasashen yamma sun isa a birnin Brussels, inda suke halarwar wasu taruruka har guda uku game da batun Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Haduwar ta hada har da ta shugabannin kasashen da ke mambobin kungiyar tsaro ta Nato domin duba matakan da suka dace su dauka domin mayar wa Rasha martani kan mamayar da ta ke yi a Ukraine.

Taron wanda shugaban Amurka Joe Biden ke halarta ana ganin cewa yana cikin tarurruka mafi muhimmanci a tarihin kungiyar.

Sai taron kasashen 7 mafiya karfin tattalin arziki a duniya na gungun G7 sai kuma wani taro na shugabannin kasashen yankin Turai.

A wani sakon bidiyo da ya fitar shugaban Ukraine, ya bukaci shugabanni da gwamnatocin kungiyar ta Nato da cewa su baiwa kasarsa makamai ba tare da wani sharadi ba, domin ceto jama’a da kuma biranen kasarsa.

Yau an shafe wata guda kenan da kasar Rasha ta abkawa Ukraine a matakin da ta ce na soji ne domin kakkabe kasar daga ‘yan Nazi.

Rasha na mai kare matakin na ta da cewa na hana Ukraine shiga kungiyar ta Nato ne da kuma zama mamba a tarayyar Turai.

Kawo yanzu dai tattaunawar kawo karshen rikicin da ake tsakanin Kiev da Moscou ta gaza cimma matsaya, inda bangarorin biyu ke zargin junansu da kawo tsaiko.

342/