Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

24 Maris 2022

16:54:17
1242080

​Rasha Ta Fidda Dalar Amurka A Matsayin Kudaden Sayen Makamashinta

Shugaban kasar Rasha Vladimir Puttin ya bada sanarwan cewa daga yanzu kasar Rasha zata sayarwa kasashen da suka dora mata takunkuman tattalin arzikin makamashinta ne da kudaden kasar wato Rouble na Rasha.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kasashen turai dai sun dogara da kasar Rasha don samun makamashi daga iskar gas da kuma man fetur har zuwa kashi 4o% na bukatunsu.

Amma bayan aikin sojen da Rasha ta fara a Ukrain a cikin watan da ya gabata, kasashen na Turai sun dorawa kasar ta Rasha takunkuman tattalin arziki daga ciki har na sayan makamashi daga wajenta.

Banda haka shugaba Putin ya bukaci babban bankin kasar ta kammala shirye-shirye don fara sayan makamashin kasar da kudaden kasar a duk wani kontaragin da za’a kulla da wadannan kasashe nan gaba.

Har’ila gwamnatin kasar Jamus ta dakatar da aikin hada kasar da butitun iskar gas na kasar Rasha wanda ake kira Nord Sream bayan fara yaki a Ukrain. Idan an kammala aikin, rasha zata ninka yawan iskar gas da take aikawa kasashen na Turai a farashi mai rasusa. A halin yanzu dai farashin cubic Lita 1000 a kasashen Turai ya kai $1,350.

342/