Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

21 Maris 2022

22:36:21
1241365

​Zanga-Zangar Adawa Da Nuna Wariya Da Zalincin ‘Yan Sanda

Dubban mutane ne a wasu garuruwan Faransa suka gudanar da zanga-zanga a karshen mako, domin nuna adawa da wariyar launin fata da kuma zaluncin 'yan sanda a sassan kasar ciki har da birnin Paris da lamarin ke ci gaba da tsananta.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, a birnin Paris, masu zanga-zangar sun yi dandazo rike da allunan da ke dauke da rubutun yin tir da zaluncin ‘yan sanda a tsakiyar birnin” yayin da wasu ke rike da wasu allunan nuna adawa da nuna wariyar launin fata, inda aka rubuta "Black Lives Matter".

Masu zanga-zangar da dama ne suka yi jawabi a filin gangamin, inda suka labarta yadda wasu daga makusantansu ko dai suka rasa rayukansu ko kuma suka fuskanci cin zarafi a hannun ‘yan sandan kasar.

Alkaluman ma'aikatar harkokin cikin gida a Faransar sun nuna cewa mutane dubu 2 da 100 ne suka shiga zanga-zangar a jiya, yayin da masu shirya gangamin suka ce sun tattara mutanen da yawansu ya kai akalla dubu 8 zuwa 10.

Ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce an gudanar da zanga-zangar a garuruwa goma sha daya na kasar.

342/